1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kwango: Tshisekedi na dab da samun nasara

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 29, 2023

Sannu a hankali an fara sakin sakamakon farko na zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyya Kwango, zaben da aka gudanar a ranar 20 ga wannan wata na Disamba mai cike da rudani.

https://p.dw.com/p/4ahw9
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Zabe | Tazarce | Shugaban Kasa | Felix Tshisekedi
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: AFP

Sakamakon baya-bayan nan da Hukumar Zaben Kasar mai Zaman Kanta CENI ta fitar dai, na nuni da cewa Shugaba Felix Tshisekedi da ke neman tazarce na gaban abokan takararsa 18 da kusan kaso 78 na kuri'u miliyan 12 da dubu 500 da aka rigaya aka kidaya. Babban dan kasuwa Moise Katumbi na matsayi na biyu da kaso 17 cikin 100, kana tsohon shugaban Hukumar Makamashi Martin Fayulu na matsayi na uku da kaso hudu cikin 100 na kuri'un da aka kidaya a mazabu dubu 46 da 422 cikin kimanin dubu 76 da aka kada kuri'un a cikinsu. Yayin zaben dai an samu matsaloli da dama da suka janyo aka kara wa'adin kada kuri'a, wanda hakan ya sanya 'yan adawa ke nuna tantama kan sahihancinsa tare da bukatar a sake gudanar da shi.