Tsofuwar ministar man Najeriya na fuskantar bincike
May 3, 2016Jami'in na hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren, ya ce masu bincike sun fara gudanar da bincikensu kan tsofuwar ministar man fetir din kasar ta Najeriya Diezani Alison-Madueke, da ake zargi da bada cin hanci na miliyoyin daloli ga wasu jami'an hukumar zaben kasar ta INEC domin su sauya sakamakon zaben da aka yi na shugaban kasa wanda ya gabata a Najeriya.
Har ya zuwa bara ma dai uwar gida Alison-Madueke na a matsayin ministar man fetir din kasar ta Najeriya a gwamnatin tsofon Shugaban kasar Goodluck Jonathan da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da ya gudana a watan Maris 2015 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasara a kai.
Kafofin yada labaran kasar da dama dai sun ce, ana zargin hukumar zaben ta INEC da laifin karbar wasu kudade da yawansu ya kai miliyan 115 na dala kwatankwacin Euro miliyan 100 daga kudaden man fetir din kasar domin su karkata akalar zaben don bai wa jam'iyyar PDP nasara, kuma da dama daga cikin wadanda suka karbi wadannan kudade na cikin hannun hukuma.