1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jami'in Saudiyya ya yi zargin barazana

October 25, 2021

Tsohon babban jami'in leken asirin Saudiyya Sa'ad al-Jabri ya yi kira ga gwamnatin Amirka ta sanya baki Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman ya sako masa 'ya'yansa da Saudiyya ta tura gidan kaso.

https://p.dw.com/p/428Q0
Saudi Arabien | Kronenprinz Mohammed bin Salman
Hoto: Depo Photos/abaca/picture alliance

A cikin wata hira da Saad al-Jabri ya yi a ranar Lahadi daga kasar Kanada, ya yi zargin cewa Mohammed Bin Salman ya koma barazana ga mutanen Saudiyya.

Jami'in leken asirin ya kasance hadimi na musamman ga tsohon Yariman Saudiyya Mohammed Nayef wanda Bin Salman ya karbe mukamin daga gare shi a shekara ta 2017. Sai dai kuma daga baya Saad al-Jabri ya yi gudun tsira da rai zuwa Kanada bayan da ya yi zargin sabon yarima Mohammed Bin Salman ya so ya halaka rayuwarsa a shekara ta 2019.

A shekarar da ta gabata ce dai wata kotu a Saudiyya ta kama 'ya'yan al-Jabri guda biyu da laifin safarar kudade ba bisa ka'ida ba tare da yunkurin guduwa daga kasar a asirce. Tun a lokacin kuma sun musanta zarge-zargen.