1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon lauyan Trump ya yi fallasa

Yusuf Bala Nayaya
August 22, 2018

Tsohon mai taimaka wa Shugaba Donald Trump na Amirka Michael Cohen, ya amsa laifi na tuhuma takwas da ake masa ciki har da taka dokar da ta shafi daukar nauyin harkokin zabe.

https://p.dw.com/p/33XHX
USA - Ermittlungen zur Russland-Affäre - Trumps Ex-Anwalt Michael Cohen
Michael Cohen tsohon lauyan TrumpHoto: picture alliance/Zuma Wire/Go Nakamura

Michael Cohen ya amince da aikata manyan laifukan takwas a ranar Talata cikin har da saba dokokin yakin neman zabe biyu bayan da ya cimma yarjejeniya da masu gabatar da kara a birnin New York.

Cohen tuni ya amince da amfani da kudin yakin neman zabe don ba da kudin toshiyar baki ga kwararriyar mai shirya fim din badalan nan Stormy Daniels wacce ke ikirarin cewa tana da alaka da ta shafi harkoki na rashin da'a da Shugaba Trump. Sauran batutuwan da ake tuhumar Cohen da su sun hadar da aikata ba daidai ba kan harkokin bankuna da haraji. Wannan bayani da Cohen ya yi cewa ya aikata laifukan na iya sawa ya share watanni daga 36 zuwa 60 a gidan kaso.