1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon ministan harkokin wajen Jamus ya rasu

Salissou BoukariApril 1, 2016

Hans-Dietrich Genscher da ke zaman ministan harkokin wajen Jamus na farko bayan hadewar kasar ya rasu yana dan shekaru 89 da haihuwa.

https://p.dw.com/p/1INvG
Berlin Gedenkveranstaltung 25. Jahrestag Unterzeichnung Zwei-plus-Vier-Vertrag Genscher
Hoto: picture-alliance/dpa/. Nietfeld

Allah ya yi wa tsohon ministan harkokin wajan kasar Jamus Hans-Dietrich Genscher dan shekaru 89 da haihuwa rasuwa da yammacin ranar Alhamis sakamakon bugon zuciya a gidansa da ke Wachtberg-Pech kewaye da iyallansa a cewar wata sanarwa ta ofishinsa. Tsohon ministan wanda ya taka rawar gani a fuskar diflomasiyyar kasar ta Jamus kusan shekaru 20 da kuma batun dunkulewar kasar a matsayin kasa daya, ya kasance ministan harkokin wajen kasar ta Jamus na farko bayan da ta dunkule a matsayin kasa daya.

Yayin da ya samu labari yana cikin wani taron manema labarai, mai magana da yawun Angela Merkel Shugabar gwamnatin Jamus, ya yaba jan kokarin da marigayin ya yi a lokacin baya, wanda ya kira babban mai kishin Turai da kuma kasarsa ta Jamus musamman ma a fannin inganta tarihin kasar ta Jamus.