1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf ya rasu

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
February 5, 2023

Rundunar sojan Pakistan ta sanar da rasuwar Janar Pervez Musharraf tsohon shugaban kasar a wani babban asibiti da ke Dubaï bayan ya yi fama da rashin lafiya.

https://p.dw.com/p/4N7IS
Tsohon shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf
Tsohon firaministan Pakistan Pervez Musharraf Hoto: Lefteris Pitarakis/AP/picture alliance

Marigayi Musharraf mai shekaru 79 a duniya ya shafe shekaru fiye da 10 yana mulkin Pakistan, bayan kwace mulki daga gwamnatin farar hula a shekarar 1999. Rundunar sojan Pakistan ce ta sanar da mutuwar tsohon shugaban a cikin wata sanarwar da ke cewa. "Allah jikan mamaci, ya kuma ba wa iyalansa jimirin rashi."

Rawar da Pervez Musharraf  ya taka a aikin soja 

An haifi Pervez Musharraf a shekara 1943 a birnin New Delhi na India, yana da shekaru hudu mahaifansa suka kaura zuwa cin rani da Musulmai ke yi a sabuwar kasar Pakistan.

Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf 
Tsohon shugaban Pakistan Pervez Musharraf Hoto: Zia Mazhar/AP/picture alliance

Pervez Musharraf ya shiga aikin soja tun yana dan shekaru 18, ya jagoranci bataliyar sojan kundun balan kasar. A shekarar 1999 ya karbi mulki da tsinin bindiga daga gwamnatin Nawaz Sharif, bisa rikicn yankin Cachemire da ya barke a tsakanin Pakistan da Indiya.

Ya kasance babban abokin dasawar Amirka bayan harin 11 ga watan Satumba na 2001, wanda hakan ya ba wa gwamnatinsa kima da samun karbuwa a wajen kasar, duk da yake ta mulkin soja ce, ya kuma shiga yakin ta'addancin Amirka gadan-gadan.

Gwamnatinsa ta yi tagomashi ga masu zuba hannun jari na ketare, ya samu damar aiwatar da sauye-sauye, sai dai daga karshe ya fuskanci matsin lamba a cikin gida.

Burin Musharraf ya kasa cika na zama dan majalisa
Jam'iyyar Pervez Musharraf ta sha kaye a babban zaben 2008 bayan ya shafe shekaru 11 yana mulkin Pakistan, ya yi barazanar rusa majalisar dokoki, matsin lamba ya tilasta masa yin murabus inda ya samu mafakar siyasa a Ingila.

Masu adawa da shugaba Pervez Musharraf
Masu adawa da shugaba Pervez Musharraf Hoto: AP

Ya sake neman kujerar dan majalisar dokoki a Pakistan bayan komawarsa gida a shekarar 2013 ba tare da ya yi nasara ba. 

A shekarar 2016 an ba shi izinin fita zuwa Dubaï, shekaru uku wata kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai bisa tuhumarsa da cin amanar kasa, sai dai daga bisani wata kotu ta wanke shi daga aikata laifukan.