Majalisa ta sa ranar zaman tsige Trump
January 23, 2021A ranar 8 ga watan Fabrairun 2021 ne majalisar ta amince ta fara zaman, bayan cimma yarjejeniyar jinkirta lokacin da jam'iyyar Republican ta nema, domin ba wa lauyoyin Trump damar yin shiri. Trump zai zama tsohon shugaban Amurka na farko da za a fara zaman hukunta shi kan laifi bayan barinsa kujerar mulki.
Kasa da mako guda da Trump ya bar mulki ne majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyar democrat suka nuna bukatar tsige shi kan zargin yi wa dimukuradiyya zagon kasa, sai dai yunkurin bai cigaba ba saboda majalisar dattijan na hutu a lokacin da aka yi dambarwar.
Amma duk da haka 'yan majalisar dokokin na alfahari da cimma burinsu na amince wa da tsige Trump har sau biyu cikin shekaru hudu, matakin da ke zama irinsa na farko kan wani shugaba a kasar. Sai dai Trump ya zargi 'yan majalisar da kunyata dimukuradiyyar Amurka ta hanyar neman tsige shi, ya kuma yi tir da aika-aikar da wasu da ke ikirarin magoya bayansa ne suka yi a zauren majalisar.