Tuhumar harin taáddanci a London
July 14, 2007Jamián tsaro sun gabatar da tuhuma a hukumance akan likitoci biyun da aka kama bisa yunƙurin harin da bai yi nasara ba, a biranen London da Glasgow. Ana tsare da mutanen biyu ɗaya a London ɗayan kuma a Australia. Yan sandan Britaniya sun tuhumi Sabeel Ahmed mai shekaru 26 da haihuwa da laifin rashin baiwa jamián tsaro bayanai wanda ka iya taimakawa wajen hana aukuwar harin taáddancin. A halin da ake ciki ɗan uwan Sabeel, wato Kafeel Ahmed wanda a yanzu yake ƙarkashin kulawar jamián tsaro a asibitin da yake kwance, bayan da ya sami mummunan ƙuna a lokacin da ya afka da motar sa ginin tashar saukar jiragen sama na Glasgow. A can Austarlia kuma yan sanda sun gabatar da Mohammed Haneef likita ɗan ƙasar India, mai shekaru 27 da haihuwa a gaban kotu a birnin Brisbane bisa tuhumar sa da taimakawa ƙungiyar yan taádda. Kotun ta bada umarnin cigaba da tsare shi har ya zuwa ranar litinin lokacin da zaá saurari buƙatar sa ta neman beli.