1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da kisan da 'yan Nazi suka aikata kan tsirarun kabilu

October 24, 2012

A birnin Berlin na Jamus an kaddamar da wani ginin tarihi domin tunwa da kisan da 'yan Nazi suka yi wa 'yan kabilun Roma da Sinti

https://p.dw.com/p/16Vmr
Hoto: picture alliance/dpa

A dangane da haka an gudanar da wani buki da ya samu halartar shugabbanin wadannan kabilu na kasa da kuma jiha cikinsu har da Romani Rose shugaban babbar hukumar wadannan kabilu. Akwai kuma wasu mutane 100 da suka tsira daga kisan kiyashin da 'yan Nazi suka yi wa Yahudawa da su kuma suka halarci bukin. Dani Karvan ma'aikacin fasaha daga kasar Isra'ila shi ne ya shirya wannan abin tarihi. Su dai 'yan kabilun Sinti da Roma kamar dai Yahudawa da 'yan luwadi sun shafe kusan shekaru 20 suna shirin girka wani abin tarihi da zai tunasar game da kisan kiyashin da 'yan Nazi suka aikata. Gwamnatin Tarayyar Jamus ce ta ba da Euro miliyan biyu da dari takwas domin gudanar da wannan buki.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu