1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yancin 'yan jarida a Jamhuriyar Nijer

Mammane Kanta/YBNovember 4, 2015

Shagulgulan bikin na bana tawagar tashar DW da ta kunshi wasu manyan jami'ai za ta je birnin Yamai fadar gwamnatin jamhuriyar Nijer don halartar bikin.

https://p.dw.com/p/1GzVl
DW im Niger Yahouza Sadissou Mabobi
Yahouza Sadissou Mabobi ministan sadarwa a NijerHoto: DW/M. Kanta

A jamhuriyar Nijer ranar 30 ga watan Nuwamba 2011 rana ce da shugaban kasar Mahamadu Isufu, ya sa hannu a kan yarjejenyar alkawarin ba za a sa dan jarida kaso ba a kan laifin aikin jarida. Wanda ya sa aka dauki ranar ta zama ranar 'yancin jarida a Nijer. A duk shekara ana shagulgulan zagayowar wannan ranar.

Shagulgulan bikin na bana tawagar tashar DW da ta kunshi wasu manyan jami'ai tashar za ta je birnin Yamai fadar gwamnatin jamhuriyar Nijer don halartar bikin.

An dai shirya gasa a tsakanin 'yan jaridar da baje koli da sauran wasanni iri-iri da aka tsara karkashin ofishin ministan sadarwa a jamhuriyar ta Nijer.

Fatimata Gali Adam ita ce babbar sakatariya a ofishin ministan sadarwa kuma shugabar kwamitin shirya wannan biki ta yi karin haske kan shirin bikin wannan rana ta 'yan jarida kamar haka:

DW - Yahouza Sadissou und Peter Limbourg
Yahouza Sadissou da Peter Limbourg shugaban DWHoto: DW/T. Mösch

"Muna ci gaba da shirye-shirye kuma akwai kananan kwamitoci baya ga wannan babban kwamiti dan a ci gaba da shirye-shirye a ba wa wannan rana babban muhimmancinta"

Tuni dai aka yi shelar gasar da 'yan jarida za su shiga daga kafafan yada labarai na rediyo da talabijin da mujallu kuma za a rufe karbar takardun shiga wanan gasa a ranar 13 ga watan nan na Nuwamba da muke ciki sannan a ranar 14 ga wata alkalai su zauna dan duba jarabawar.

Zubairu Musa dan jarida ne a Nijer da ya kai takardarsa ofishin ministan sadarwar inda anan ne ake karbar takardun 'yan jarida da dama da suka shiga wannan gasa. Ya kuma yi karin haske kan abin da ake tsammani su rubuta a gasar.

Nelson Sul d'Angola
Dan jarida a fagen aikiHoto: DW/N. S. d'Angola

"Abin da ake bukata shi ne yadda dan jarida zai rubuta rahoto cikakke ba tare da daukar bangare ba saboda kwarewa a aikin".

A ranar talatin ga watan Nuwamba ne a babban filin wasa na Palais des Congre`s na birnin Niamey kafafan yada labarai za su baje kolin kayayyakinsu inda anan ne ma gidan rediyon DW za su kafa tasu rumfar da nuna ci gaban fasaharsu a fagen yada labarai kuma a nan ne ma za su bada babbar kyauta cikin kyautukan da masu gasa 'yan jarida za su ci baya ga sauran kyaututtuka da za a samu a wannan rumfa.