Tuni da harin nukiliya kan Nagasaki
August 9, 2021A wannan rana ta 08.09. 2021Japan ke tuni da kazamin harin nukiliya da Amirka ta kai kan birnin Nagasaki shekaru 76 da suka gabata. Inda mutum sama da dubu saba'in suka rasa rayukansu a yini guda. Amirka ta soma jefa makamin Nukiliya na kare dangi a birnin Hiroshima kafin ta jefa na biyun a Nagasaki, lamarin da ya sa Japan mika wuya a yayin yakin duniya na biyu.
Duk da cewa, annobar corona ta rage wa taron da aka saba gudanarwa a duk shekara armashi, wadanda suka tsira daga harin da kuma wasu daga 'yan kasashen waje sun gudanar da addu'oi tare da yin tsit na minti guda a daidai karfe 11.02 biyu wato lokacin da Amirka ta jefa makamin karshe.
Magajin garin Nagasakin Tomihisa Taue, ya ce ya zama wajibi shugabanin kasashen duniya, sun hada kai don ganin an cimma yarjejeniyar haramta kera makaman na kare dangi. Tarihi ya nuna cewa, hare-haren na Hiroshima da Nagasaki sun kasance karon farko da ake kai hari da makami mai guba kan bil'adama a duniya.