1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya: Shekaru 7 da boren juyin juya hali

Abdullahi Tanko Bala RGB
January 15, 2018

Shekaru 7 bayan boren da aka fara a Tunisiya wanda ya rikide ya zama boren juyin juya hali a kasashen Larabawa, a cewar 'yan kasar har yanzu babu abin da ya sauya game da bakar wahalar da jama'a ke sha.

https://p.dw.com/p/2qrbv
Tunesien - Versammlung von Gewerkschaftsmitgliedern
Gangamin masu zanga zanga a TunisiyaHoto: UGTT

Ga mutane da dama a Tunisiya rayuwa na kara yin tsauri, baya ga tsadar Burodi da ke kara hauhawa da kayan masarufi da suka yi tashin gwauron zabi, a yanzu gwamnati ta yi karin kudin haraji. Matsalar ma dai ba ta tsaya a nan ba, ga rashin aikin yi da ya addabi matasa, sannan ga cin hanci da rashawa da ya yi katutu hade da abin da 'yan kasar suka kira rashin ingantattun manufofin tattalin arziki daga bangaren gwamnatin.

Tunesien Protesten gegen die Regierung in Tunis
Al'ummar kasar sun zargi shugaba Beji Caid Essebsi da gazawaHoto: DW/S. Mersch

Wadannan matsaloli sun sa 'yan Tunisiya yin tababa akan tasirin mulkin dimokradiyya a kasar. Rashin aiki a tsakanin matasa ya yi kamari fiye da shekarun baya, kusan kashi 35 cikin dari na matasan kasar basu da ayyukan yi. A ranar Lahadin da ta gabata, masu zanga zangar karkashin tsauraran matakan tsaro sun yi gangami suna cewa "tir da talauci da yunwa".Tun bayan murabus din tsohon shugaban kasar Zine el Abidine Ben Ali a ranar 14 ga watan janairu bisa matsin lambar juyin juya hali a shekarar 2011, 'yan kasar sun yi amfani da zanga zangar ta wannan watan domin nuna kudirinsu na neman sauyi.

Kudin kasar na Dinar ya fadi kasa warwas.

Matsalar kudi da tattalin arziki a Tunisiya
Matsalar kudi da tattalin arziki a TunisiyaHoto: picture alliance / abaca

Tattalin arzikin Tunisiya dai ya tabarbare tsawon shekaru. A shekarar 2017 arzikin da kasar ke samu a shekara ya karu ne da kashi daya tal cikin dari, a lokaci guda kuma farashin kayayyaki sun yi tashin gwauron zabi da kimanin kashi shida cikin dari. Wannan hali dai ya fi shafar masu karamin karfi. Tashin farashin kayayyaki da karin haraji sun sa lamarin ya tabarbare yadda jama'a ba za su iya jurewa ba. Musamman dai jama'a na nuna bacin ransu ne sakamakon tafiyar hawainiyar da gwamnatin ke yi wajen aiwatar da sauye sauye da za su inganta rayuwar 'yan kasa. Tabargazar cin hanci da ta yi katutu da nuna son kai. Sarkakiyar tafiyar da gwamnati da aringizon kudi su ne ke lakume rabin kasafin kudin kasar, yayin da a waje guda kuma aka wawashe baitulmalin gwamnati.Tun shekarun da suka wuce zuwa yau, kasar ta Tunisiya na dogara ne da tallafi daga kasashen duniya masu bada agaji.