Ana son Taliban ta mutunta mata
August 18, 2021A sanarwar hadin gwiwa da suka sanya ma hannu a wannan Laraba, sun yi kira ga Taliban kan ta inganta rayuwar wadanda ake wa kallon mafi rauni a cikin al'umma, ta hanyar ba su damar yin aiki da bidar ilimi da kuma ba su gwargwadon 'yancin walwala.
Kiran da suka yi baya rasa nasaba da zargin tauye 'yancin mata da yara da aka zargi Kungiyar Taliban da yi a lokacin mulkinta kafin a hambarar da gwamnatin kungiyar. Sun kuma baiyana damuwarsu a game da hali na rashin tabbas da rayuwar mata da kuma kananan yara za su kasance a halin da kasar ta Afghanistan ta tsinci kanta a yanzu.
A daya bangaren kuwa, wani sabon rahoto daga kasar ta Afghanistan, na cewa mutum uku sun mutu wasu shida sun ji rauni, a yayin da Taliban ta yi kokarin tarwatsa dandanzon masu zanga-zanga da kwace ikon da ta yi a yankin gabashin kasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabanin Kungiyar Taliban da suka yi gudun hijira, suka soma komawa kasar don shirin kafa gwamnati.