Turkiya ba zata kai hari kan ´yan tawayen Kurdawa a cikin Iraƙi ba
June 12, 2007Talla
FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya kawad da yiwuwar kaddamar da wani farmakin soji akan ´yan tawayen Kurdawa a arewacin Iraqi. A lokacin da yake magana da ´yan jarida gabanin wani taron manyan jami´an tsaro Erdogan ya jaddada cewar daukar matakin soji zai zama zabi na karshe. FM na Turkiya ya ce yana shirin yin tattaunawa da takwaransa na Iraqi Nuri al-Malik akan wannan batu. Ya ce gwamnati a birnin Ankara na mayar da hankali kan yakar ´yan tawaye dake cikin yankin kasar Turkiya. Da farko hafsoshin sojin kasar sun ce ana bukatar daukar matakan soji don murkushe ´yan tawayen jam´iyar Kurdawa ta PKK dake arewacin Iraqi. Amirka da Iraqi na nuna matukar adawa da kowane irin kutse sojojin Turkiya cikin Iraqi.