Turkiya ta lashi takobin ganin bayan 'yan tawayen PKK
October 20, 2011Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya bi sahun ƙungiyar Tarayyar Turai EU da ƙasar Amirka da kuma ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO wajen yin tir da kisan sojojin Turkiya 24 da 'yan tawayen ƙungiyar Kurdawa ta PKK suka yi. Ya ce ba za a amince da hare haren da Ƙurdawan ke kaiwa ba, inda ya yi kira da girmama 'yancin kan yankunan ƙasashen Iraƙi da Turkiya. Ƙasar Turkiya dai ta ƙaddamar da wani gagarumin farmakin sojojinta a arewacin Iraƙi biyo bayan hare haren da Ƙurdawan suka kai a ranar Laraba, dake zama mafi muni a cikin sama da shekaru uku. An yi imanin cewa an kashe 'yan tawaye 20. Tarayyar Turai da kuma Amirka sun sanya sunan ƙungiyar PKK a jerin sunayen ƙungiyoyin 'yan ta'adda a duniya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu