Gwamnatin Turkiyya na bincike kan mutuwar 'dan jarida
October 21, 2018Talla
Bayan da kasar Saudi Arabiya ta tabbatar da rasuwar 'dan jaridar a ofishin jakadancin ta da ke birnin Istanbul kakakin jam'iyyar AKP mai mulki a Turkiyya, ya bayyana cewar gwamnatin kasar ba ta da niyyar dora alhakin wannan mummunan al'amari a kan wani to amma fa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana abin da ya faru a fili ba.