1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Khashoggi :Shirin binciken kasa da kasa

Gazali Abdou Tasawa
December 11, 2018

Kasar Turkiyya ta sanar da soma tattaunawa da MDD kan batun yiwuwar kaddamar da binciken kasa da kasa kan batun kisan dan jaridar nan na kasar Saudiyya Jamal Khashoggi

https://p.dw.com/p/39slb
Türkei, Ankara: Mevlut Cavusoglu, Außenminister aus der Türkei, spricht nach einem Treffen mit dem US-Außenminister Pompeo
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Ozdel

Ministan harakokin wajen kasar ta Turkiyya Mevlüt Cavusoglu ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai a wannan Talata a birnin Ankara, ya kuma yi karin bayani a game da dalillansu na daukar wannan mataki yana mai cewa:

"Mutanen da suka aikata wannan laifi a gaban kotun Turkiyya ce ya kamata a gurfanar da su, to amma Saudiyya ta kiya. A kan haka ne muka tattauna da Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya da wasu manyan kasashe kan yiwuwar gudanar da bincike na kasa da kasa kan lamari"

Minista Cavusoglu ya ce a daura da taron G20 ne da ya gudana a farkon wannan wata na Disamba a ya tattauna da wasu takwarorinsa na kasashen duniya da suka hada da kasar Kanada kan wannan batu inda suka ye suna son yin baki guda wajen shigar da wannan bukata.