1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Erdogan ya lashe zabe tun a zagayen farko

Salissou Boukari
June 25, 2018

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ke neman wani sabon wa'adin mulki a kasar ya sake lashe zaben shugaban kasar da kimanin kashi 52,5%, sannan ya samu rinjaye a majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/30Csa
Wahlen Türkei - Erdogan erklärt sich zum Sieger
Hoto: picture-alliance/AA/M. Kaynak

Sakamakon ya nunar da cewa jam'iyyar AKP ta Shugaba Erdogan da kuma abokiyar kawancenta ta MHP sun samu rinjaye a majalisar dokoki da kashi 53,6 a cewar shugaban hukumar zaben kasar ta YSK Sadi Güven yayin wani taron manema labarai da ya gudanar. Da yake magana a gaban dubban magoya bayansa tun a daren jiya, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yaba wa illahirin 'yan kasar ta Turkiya miliyan 81 da suka yi zabe yana mai cewa:

"Daga gobe za mu soma aiki domin cika alkawurran da muka dauka wa al'ummarmu, kuma mun kammala shirye-shirye kan abun da ya shafi sabon tsari na shugaban kasa mai cikeken iko. Turkiyya kuma ta kudiri aniyyar yaki da duk wata kungiyar 'yan ta'adda, har da kungiyar PKK da ta FETO, tare da ci gaba da kakkabe miyagu a kasar Siriya, don baiwa bakinmu damar komawa gidajensu."

Babban mai hamayya da shugaba Erdogan Muharrem Inc, ya samu kashi 30,7 cikin 100, sannan hadin gwiwar 'yan adawa sun samu kashi 34 cikin 100 a majalisa a sakamakon da kamfannin dillancin labaran kasar na Anadolu ya wallafa.