Turkiyya na son Amurka ta sa baki don tsagaita wuta a Gaza
November 6, 2023A yayin ganawar da jami'an biyu suka yi a ranar Litinin (06.11.2023), Mista Hakan Fidan ya jaddada wa takwaransa na Amurka Antony Blinken cewar ya zama wajibi a dakatar da Isra'ila kan hare-haren da ta kai wa kan mai uwa da wabi a Gaza, sannan kuma ya kamata a tsagaita wuta take yanke.
Karin bayani: Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce adadin Falasdinawan da hare-haren Isra'ila suka hallaka ya haura dubu tara
To sai dai daga nasa bangare mista Blinken ya ce a baya-bayan nan an samu babban ci gaba a game da shigar da karin kayan agaji zirin na Gaza, sannan kuma Washington ta bukaci Isra'ilar da ta takaita hare-haren da ta kai wa wadanda ke janyo asarar rayukan fararen hula.
Karin bayani: Kungiyoyin agaji na kiran da a kawo karshen luguden wuta a Zirin Gaza
A baya dai Amurka da ke zama abokiyar huldar Isra'ila ta farko a ta fuskar siyasa da kuma soja ta nuna adawa ga matakin tsagaita bude wuta a Gaza sai dai amma ta goyi da bayan dakatar da hare-hare na dan lokaci domin ba da damar isar da kayan agaji da suka makale a iyakar Masar i zuwa zirin.