1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turmutsitsi ya yi ajalin masu karbar kyautar abinci a Abuja

December 21, 2024

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce akalla mutane 10 ne aka tabbatar da mutuwarsu kawo yanzu. Kakakin 'yan sandan a Abuja Josephine Adeh ta ce cikin wadanda suka rasa rayukan nasu akwai kananan yara guda hudu.

https://p.dw.com/p/4oTA8
Hoto: Greg Baker/AP Photo/picture alliance

Mutane masu yawa sun rasa rayukansu a yayin wani turmutsitsi da ya faru a wajen rabon kyautar kayan abincin Kirsimeti a wata coci da ke Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

Tuni dai shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya soke halartar wasu bukukuwan karshen shekara da ya so halarta a wannan Asabar domin nuna alhini da girmama rayukan mutanen da suka mutu a turmutsitsin na neman kyautar abincin. Shugaban na Najeriya ya ce duk da cewa wannanlokacina murna da nuna kaunar juna ne, amma  rasa rayuka da aka yi ya girgiza shi matuka, yana mai fatan samun salama ga wadanda suka rasa rayukan nasu.