1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta fusata da yanke alakar da Nijar ta yi da ita

August 8, 2024

Ukraine ta ce ba ta ji dadin yanke alakar diflomasiyya da Nijar ta yi da ita ba, 'yan kwanaki bayan da makwabciyar Nijar, Mali ta dauki irin wannan mataki bisa zargin sojojin Ukraine da tallafa wa 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/4jFMN
Hoto: UKRAINIAN PRESIDENTIAL PRESS/REUTERS

Ma'aikatar harkokin wajen Ukraine din ta ce ta yi takaicin yadda mahukuntan Nijarsuka yanke shawarar dagula alakar diflomasiyyar da ke tsakaninsu ba tare da sun gudanar da wani bincike kan gaskiyar abin da ya faru da jami'ansu da hukumomin Mali ba. Gwamnatin na Ukraine a sanarwar da ta fitar ta bakin ma'aikatar kula da harkokin wajenta a Alhamis din nan ta ce wadanda suka zarge jami'anta da taimakon 'yan ta'adda sun gaza fito da hujjojin da ke tabbatar da ikirarin da suke yi.

Kasashen Nijar da Mali da dukkaninsu ke karkashin mulkin soji sun koma alaka da sojojin Rasha domin maye gurbin dakarun kasashen yamma da sojojin suka raba gari da su.