Tasirin rikicin Boko Haram a Najeriya
June 24, 2021Wannan dai shi ne karon farko da wadannan Jakadun kasashe da ke kan gaba wajen bada kudaden tallafi domin karfafa ayyukan jin kai suka ziyarci yankin. Wannan rahoto da Asusun raya kasa na Majaliasar Dinkin Duniya ya kaddamar a Maiduguri ya Kunshi cikakkun bayanai kan irin barnar da rikicin Boko Haram ya haifar wanda aka kwashe tsawon shekaru 12 ana fama da shi.
Rahoton ya yi bayanai kan rayukan da aka rasa da dukiyoyi gami da kadarori na makudan kudade da yadda rikicin ya raba miliyoyi da matsagununsu da kuma yadda ya haifar da koma baya ga samar ilimi da rayuwa da koma bayan tattalin arzikin wanann shiyya. Haka kuma rahoton ya fayyace dalla dalla irin tallafi na taimako jin kai da aka aiwatar da ma kokarin sake tsugunar da mutane da samar musu da abinci da kokarin ilmantar da miliyoyin yara da basu samu zuwa makaranta ba.
Da ya ke tsokaci kan rahoton babban jami’in da ke kula da ayyukan jin kai na Majalalisar Dinkin Duniya a Najeriya Mr Edward Kallon ya ce rahoton ya hadu duk dai da cewa har yanzu akwai abubuwan da ake nema a bankado in ana son magance matsalolin da ma farfado da yankin.
Ya ce ina fata da wannan aiki da UNDP ta fara za a fadada shi zuwa neman amsoshin wasu tambayoyi da suke da muhimmanci a kokarin magance wadannan matsaloli. Dole a binciko su wa ke samar da kudi ga wadan nan mayakan? A ina suke samo samun kudin? Ta ya mutane ko al’ummar Borno za su tuhumi wadannan mutane? Wadannan muhimman tambayoyi ne da su ke neman Amsa.
Shi kuma Mr Nicolas Simard Jakadan kasar Kanada a Najeriya wanda ya yi Magana da manema labarai a madadin sauran Jakadu ya bayyana damuwa kan halin da ake ciki da matsalolin yunwa da ke addabar shiyyar.
Ya ce abin takaici da tashin hankali da muka shaida shi ne akwai karuwar hare-hare da Kungiyar ISWAP da ke kai wa kan fafaren hula da masu aikin jin kai a ‘yan watanin nan. Wannan Abun tashin hankali ne. Za mu bada goyon baya domin a kawo karshen wannan zubar da jini. Haka kuma akwai barazanar fari da ke fuskantar wannan yankin. Kasashen G 7 sun tattauana a taron da suka yi a kai kuma za su bada tallafi na kudi da duk abin da ya kamata domin a magance matsalar.
Gwamman jihar Borno Farfesa Bagana Umara Zulum ya jinjinwa Asusun na UNDP saboda kokarin binciko wadannan matsaloli da ma samar da mafita ga halin da ake ciki a wannan sashi na duniya. Sai dai gwamnan ya ce akwai bukatar masu bada tallafin su hada kai da gwamnatin jihar Borno saboda yadda ake zargin wasu bangarorin da karkatar da akalar kudadaen da aka bayar domin taimakawa al’umma.
Kuna sanar da gudumawar makudan kudade, amma in ba a bincika yadda ake kashe kudaden da kyau ba, ko kashi 30% ba zai isa ga wadanda aka nufa ba. Saboda haka dole mu yi aiki tare ta yadda za a aika da tallafin da aka kawo zuwa mutanen da ake so su mora. Wadannan kudade da kuke kawo na mutanen kasashenku da ke biyan haraji dole a yi gaskiya wajen kashe su. Maganar gaskiya ba sai an ambaci suna ba, cin hanci ya yi katutu a wannan aiki.
Masana da masharhanta da sauran masu ruwa da tsaki a wannan yankin na fatan cewa hukumomi za su yi amfani da wannan rahoto wajen samar da mafita ga halin da miliyoyin al’umma su ke ciki na kuncin rayuwa da bude hanyar kawo karshen kalubalen tsaro da ya hana musu rawar gaban hantsi.