UNESCO ta karrama 'yan jaridun yankin Falasdinu
May 3, 2024Hukumar ilimi da kimiya da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta bayar da lambar yabo ta 'yancin 'yan jaridu ga daukacin 'yan jaridar yankin Falasdinu da ke aikawa da rahotanni daga zirin Gaza wanda ya shafe sama da watanni shida cikin kazamin yaki sakamakon farmakin da Isra'ila ta kai a kudancin yankin.
A lokacin da yake sanar da wannan karramawa, shugaban alkalan da suka jagoranci tantance bayar da lambar yabon Mauricio Weibel ya yi jinjinar ban girma tare da karfafa gwiwa ga 'yan jaridar yankin Falasdinu da suka jajirce wajen gudanar da aikinsu duk da hadarin da suke fuskanta cikin yanayi na yaki.
Karin bayani: 'Yancin 'yan jarida ne yancin duniya
Daga nata bangare darekta janar ta Hukumar UNESCO Audrey Azoulay ta jaddada muhimmancin hada kai ta yadda 'yan jaridu a fadin duniya za su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin 'yanci da adalci.
Karin bayani: UNESCO: 'Yan jaridar da ake kashewa na karuwa
A cewar kungiyar kare hakkin 'yan jarida da ake wa lakabi da CPJ mai hedikwata a birnin New York na Amurka, akalla 'yan jarida da ma'aikatan yada labarai 97 ne aka halaka daga farkon yakin Gaza zuwa wannan lokaci, kuma 92 daga cikinsu Falasdinawa ne, yayin da wasu 16 suka jikkata.