1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNESCO ta samu shekaru 60

October 5, 2005

A yau laraba kungiyar UNESCO ke bikin cika shekaru 60 da kafuwa

https://p.dw.com/p/BwXG
UNESCO ta cika shekaru 60
UNESCO ta cika shekaru 60Hoto: Montage/dpa

Wannan sabanin ya shafi wata yarjejeniya ce dake da nufin ba da cikakkiyar kariya ga salon al’adun kowace kabila ko kuma kowane yanki a sassan duniya dabam-dabam. Kasashen Amurka da Indiya da Mexiko na adawa da wannan yarjejeniya. Kuma ko shakka babu za a tafka muhawara mai tsananin gaske a zauren taron kungiyar ta UNESCO, wanda aka fara tun a ranar litinin da ta wuce. Domin kuwa maganar ta shafi wani lamari ne na makudan kudi. Misali a can kasar Amurka kamfanonin finafinan silima da gidajen fayafaye da madabi’u na tattare da ra’ayin cewar al’adu tamkar wata haja ce ta ciniki da ba zata yiwu a dauki matakan kariya akai ba. Fadar mulkin Amurka ta White House na bukatar ganin duk wata ka’idar da za a shimfida dangane da finafinai da litattafai da fayafayan kida tayi daidai da ka’idojin da suka shafi hajojin ciniki kamar su motoci da kekuna da makamantansu. Amma a daya bangaren masu adawa da wannan manufa ta Amurka na tattare da ra’ayin cewar ba da kariya ga al’adu na gargajiya da mutane suka gada tun daga kakannin kaka abu ne da ba makawa game da shi. Kuma wannan ba magana ce kawai da ta shafi kare makomar al’adu ba, kazalika tana da nasaba da ‚yanci da walwalar dan-Adam da kuma manufofi na demokradiyya da ake tinkaho da su yanzu haka. Yin fatali da al’adun mutane na ma’anar take hakkinsu, in ji Muhammed Achaari, ministan al’adun kasar Maroko dake magana da yawun masu adawa da matsayin da kasashen Amurka da Indiya da kuma Mexiko suka dauka dangane da wannan batu, wanda kimanin wakilai dubu biyu daga kasashe 191 ke tattaunawa kansa a zauren taro na 33 na kungiyar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta MDD mai bikin samun shekaru 60 da kafuwa a birnin Paris. Kamfanonin finafinan silima da gidajen litattafai da na kida suna bakin kokarinsu wajen tuntubar mahalarta taron kai tsaye ko Ya-Allah zasu iya yin tasiri akansu domin su yi fatali da shawarar ba wa al’adu na gargajiya cikakkiyar kariyar da ta dace. A daya bangaren kuma akwai kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka dage wajen ganin cewar maganar kudi ba tayi tasiri akan kudurin da kungiyar ta UNESCO zata yanke ba. A lokacin da yake bayani game da haka Sascha Constanza Chok, wakilin wata gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu ta kasa da kasa dake halartar zauren taron ya ba da misali da kasar Haiti, inda yake cewar:

Misali a nan shi ne kasar Amurka ta gargadi kasar Haiti da cewar idan har kuna so mu kulla wata yarjejeniya ta ciniki tare da ku, to kuwa wajibi ne ku ba wa ‚yan kasuwar Amurka dake neman zuba jari a kasarku cikakkiyar dama ta sayen kafofinku na al’adu kuma gwamnati ta daina tallafa wa gidajenta na rediyo da ‚yan wasanninta na kwaikwayo da makadanta da kudi, saboda haka yayi dauira da manufar sakarwa da harkokin kasuwanci mara. A nata bangaren kasar Haiti na da ikon kin amincewa da haka saboda hannu da take da shi a yarjejeniyar kariyar al’adu ta UNESCO.