Wacce tafi kowa shekaru a duniya ta rasu a Spain
August 20, 2024Iyalanta sun ce Branyas ta shafe shekaru 20 a gidan kula da tsofaffi na Santa Maria del Tura da ke shiyyar arewa maso gabashin Spain, kafin jikinta ya tabarbare a 'yan makonnin da suka gabata, kamar yadda suka sanar a shafin X.
Karin bayani: Fatima al-Fihri: Wace ta gina jami'a mafi tsufa a duniya
Kundin adana bayanan tarihi da kuma ayyana gagarumar bajinta na duniya na Guinness World Records, ya sanar da Branyas a matsayin wacce ta fi kowa shekaru a duniya bayan mutuwar mai rike da kambun 'yar kasar Faransa Lucile Randon mai shekaru 118 da ta mutu a 2023.
Karin bayani: Dan-wasa mafi tsufa a gasar kofin Duniya
Kwararrun likitocin da suka yi bincike kan kwayoyin halittunta na Jami'ar Barcelona sun yi matukar mamakin yadda dattijuwar ke iya bada labarin abin da ya faru a lokacin da take shekaru 4 a duniya.