1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wadanda suka kai hari a London

Zainab A MohammadJuly 13, 2005

Uku daga cikin masu kai harin London sun mutu

https://p.dw.com/p/Bvar
Hoto: DW-TV

Masu bincike na kasar Britania na cigaba da gudanar da bincike dangane da hare haren boma bomai da aka afkawa birnin London dasu a makon daya gabata.

A yanzu haka dai masu bincike na mayar da hankali ne wajen gano wanda keda alhakin daukan nauyin kai wadannan hare haren wanda akayi imanin cewa wasu masu takardan kasancewa yan Britania amma haifaffun kasar Pakistan ne suka aiwatar dasu.

Jamian binciken dai sun hakikance cewa uku daga cikin wadanda ake zargin harin ya ritsa da rayukansu,harin dake zama na farkon irinsa a kasar ta Britani tun bayan yakin duniya na biyu.

To sai dai har yanzu babu masaniya dangane da makomar daya daga cikin mutane hudun, da ake zargin cewa shine ya tayar da bomb acikin daya daga cikin jiragen kasan,sai dai an cafke wani mutum a yammacin Yorkshire,inda daga nan ne sauran ukun suka fito.

A daren talata nedai yansanda suka bayyana cewa uku daga cikin mutanen da suka kai harin yan Britania ne dake da asali a Pakistan,wadanda kuma keda zama a Yorkshire ta yamma dake jihar Leeds.

Bugu da Karin sunyi imnin cewa mutane hudun,wadanda uku daga cikinsu suka iso cikin gari da jirgin kasa ranar alhamis da safiya,sun eke dauke da alhakin kai wadannan hare hare da suka kasha akalla mutane 52.

Kamar yadda yawancicin gidajen talabijin suka nunar,Yan yankin na Asia 4 sun sauka daga jiragi Thames Link ne wanda ya dauko su daga tashar Luton dauke da jakar goyo,wanda injisu ke dauke da boma boman,kafin su gangara zuwa tashar jiragen kasa ta kings Cross dake karkashin kasa.

Mutane ukun da ake zargi dai an bayyana shekarunsu da kasancewa 30 kana gudan 23 ayayinda na ukun yake 19.

A yayinda yansanda ke cigaba da binciken nasabar wadannan hare hare da suka wakana a ranar alhamis data gabata,ayau laraba an saka gabatar da sunayen wasu mutane da wadannan hare haren ya ritsa da rayukansu,domin har yanzu wasu yanuwa da abokan arziki basu san inda yan uwan nasu suke bay a zuwa yanzu ,tun bayan wadannan hadarin.

Duk dacewa ya zuwa yanzu mutane 52 akace harin ya ritsa da rayukansu,jamiaai sun sanar dacewa adadinsu zai iya karuwa ,domin gawawwaki 11 aka iya ganesu.A yanzu haka dai ana kara gabatar da sunayen mutanen da suka bace tun ranar da wadannan boma bomai suka ritsa da jiragen karkashin kasa uku,kana sa`a guda bayan nan wani bomb din ya tarwatse a wata bus mai hawa biyu dake daukan pasinjoji acikin birnin na London.