Wahalar kai agaji daga Kamaru zuwa Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
February 5, 2014'Yan kungiyar Anti Balaka da tsohowar kungiyar yan tawaye wato 'yan tawayen Seleka sun hana direbobin manyan motoci dake dauke da kayan agajin da zasu kai Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya ketara iyakar Garwa Bulai dake kasar Kamaru, a bisa hare-haren da suke kai musu wadda ya kai ga mutuwar akalla direbobi biyar.
Direbobin manyan motocci 600 da ke dauke da kayan agajin da zasu kai Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya na cikin mawuyacin hali a bisa hare-haren da 'yan kungiyar Anti Balaka da na Seleka suke kai musu, wadda ya hana su karasawa inda zasu kai kayan agajin a bisa gudun kada su rasa rayukan su.
Zamba Zru, daya daga cikin direbobin da ke fuskantar wannan matsalar yace kwanan sa 40 a karkashin motarsa:
''Alal misali ni da nake magana ɗan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne, kuma ina kwana a ƙarƙashin motata, kuna jin ina jin dadin kasancewar wannan al-amarin ne, nima ina so na koma gida wajen 'yan-uwa na ''
Direbobin suna dauke da kayan agaji ne daga tashar jiragen ruwan dake kasar Kamaru da zasu kai Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, sunyi bayani akan cewar sun makale a iyakar Garwa-Bulai ne a bisa kokarin guje ma hare-haren da yan kungiyar Anti- Balaka da na 'yan tawayen Seleka suke kai masu.
Toukour ma'aikacin saye da sayarwa ne a kasar ta Kamaru wanda ya yi bayanin cewa direbobi uku sun rasa rayukan su a bisa kokarin da suke yi wajen ƙetare iyakar domin su kai kayan agajin Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya.
"Daya daga cikin direbobin da aka kashe, a wajen muka binne shi, biyu kuma mun kaisu kauyukan su, akwai direbobin da suka sha mummunan duka wasu ma da adda aka daddatsa jikin su. Ko a yanzu da nake magana akwai direbobi hudu dake cikin mawuyacin hali a can Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiyar, gaskiya al'amarin yayi muni sosai."
Dan-Dan dan shekaru 28 direba ne, kuma yana daya daga cikin wadanda suka ketara rijiya da baya, domin kuwa motarsa tayi kaca-kaca a bisa harin da aka kai masa, amma yayi sa'a ya tsira da ransa duk da kasancewar ya samu raunuka.
"Sun kawo mana harin ba-zata a yayinda suka bude mana wuta. Kalli motocin duk da hujin harsasan da akai ta harba mana. Harsasan sun huda motocin ta ko'ina. Duk abin da ka ke gani nan harsasai ne."
Direbobin dake yawon kai kayan agajin dai sun bukaci Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya da ta tabbatar masu da tsaro domin su samu su tsira da rayukan su.
Mawallafa: Moki Kinzeka/Zainab Babbaji
Edita: Umaru Aliyu