Wai da Jamusawa a yakin basasan Siriya?
April 25, 2013A karon farko gwamnatin Jamus ta ba da tabbacin cewa akwai mayaka masu tsatsauran ra'ayin addini da suka bar kasar suka je Siriya domin shiga yakin hambarar da Shugaba Bashar al Assad. Ministan cikin gidan Jamus, Hans-Peter Friedrich ya fada wa jaridar "Spiegel Online" cewar hukumomin tsaro na nuna matukar damuwarsu game da yadda masu matsanancin ra'ayin Islama daga nan Jamus ke dunguma zuwa Siriya. Hakazalika ana fargabar cewa idan sun dawo mai yiwuwa ne su dauki makamai domin shiga yakin-bi-sabilillahi.
Gilles de Kerchove, wanda kwararren masanin ne akan ta'addanci ya ce akwai yan kishin Islama kusan dari biyar da suka bar kasashen Turai suka je Siriya domin shiga yakin da 'yan tawaye ke yi da shugaba Assad.
Mawallafi: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal