1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Tim Walz zai mara wa Kamala Harris baya

Suleiman Babayo ATB
August 6, 2024

An bayyana sunan Tim Walz a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin shugaban kasa tare da Kamala Harris ta Jam'iyyar Democrats a zaben shugaban kasar Amurka da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4jBQJ
USA Washington 2024 | Demokratis Gwamna Tim Walz
Tim Walz gwamnan jihar Minnesota wanda zai yi takarar mataimakin shugaban kasar Amurka

Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris kuma 'yar takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar Democrats ta bayyanan sunan Tim Walz gwamnan jihar Minnesota a matsayin wanda zai yi mata takarar mataimakin shugaban kasa a zaben watan Nuwamba da ke tafe. Nan gaba a wajen yakin neman zabe a Philadelphia Harris za ta gabatar da Walz ga magoya bayan jam'iyyar.

Shi dai Tim Walz gwamnan jihar Minnesota ya kasance tsohon dan majalisar dokoki mai shekaru 60 da haihuwa, wanda yake da matsakaicin ra'ayin gaba-dai gaba-dai a jam'iyyar Democrats.

Ita dai Kamala Harris ta jam'iyyar Democrats za ta fafata da Donald Trump na jam'iyyar Republican a zaben na watan Nuwamba. Duk wanda ya lashe zabe yana da karfi fada aji, saboda tasirin kasar ta Amurka wadda take kan gaba wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.