Wane ne ya mallaki rukunin gidajen da EFCC ta kama?
December 3, 2024Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma zambar kudadde ta Najeriya EFCC ta yi wannan babban kamu ne bayan daukar lokaci na bibiya da bincike a kan gidajen da kotu ta tabbatar da cewa an same su ne ta cin hanci da rashawa. Gidaje ne na kawa samfurin "duplexes" guda 753 da ma wasu gidajen na daban, amma mallakar mutum guda ne da ke zama tsohon ma'aikacin gwamnatin Najeriya, wanda EFCC ta sakaye sunansa saboda ci-gaba da bincike a kansa.
Karin bayani: Yunkurin dakile cin hanci a Najeriya na gamuwa da cikas
Dele Oyewale, da ke zama jami'in yada labaru na hukumar ta EFCC ya ce: " Gagarumin kwato kadarori na haramun da ya fi kowane girma da hukumar EFCC ta yi ya faru ne a ranar litinin 2 ga watan Disamban 2024, bayan da mai shari'a Jude Onwuegbuzie ya amince da mallaka wa gwamnatin Najeriya kadarori na gidaje sanfurin duplexes 753 da ma wasu gidaje: Wani babban tsohon jami'in gwamnati Najeriya ne ya mallaki gidajen, wanda muka sakaye sunasa a yanzu. An bi dukkanin matakan da suka dace wajen kwace gidajen don haka hallastacce ne''.
Karuwar masu halin bera a Najeriya
EFCC ta yi amfani da sashe na 44 na tsarin mulkin Najeriya wajen gudanar da wannan aiki. Amma bai hana masu fafutaka irin su Isa Tijjani da ya dade yana gwagwarmaya tofa albarkacin bakinsu a kan wannan nasara da EFCC ta yi ba. Duk ma da nasarorin da ake samu a yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, masu halin bera da ke kasara tattalin arziki da jefa al'umma cikin talauci na karuwa, lamarin da ke kara zama babbar annoba. Amma Imran Wada Nas, shugaban rundunar adalci a Najeriya ya ce: " Ba karamar barna wasu manyan jami'an gwamnati ke yi wa arzikin Najeriya ba:".
Karin bayani: Najeriya: Gwamnati na yakar cin-hanci
Hukumar EFCC ta ki bayyana sunan tsohon jami'in gwamnatin da aka karbe wadannan gidaje da ya mallaka ta haramtaciyyar hanya, amma abin da ya dauki hankali shi ne yadda hukumar ta ce bai nuna damuwa a kan karbe wadannan kadarori ba. Sai dai EFCC ta ce kayan da aka karbe sun zama mallakar gwamnati, amma a lokutan baya ana samu zargi na sake karkata da irin wadannan kadarori a yanayi na sata ta saci sata. Auwal Musa Rafsanjani na kungiyar Cislac ya ce suna yaki da wannan matsala.
A bisa dokar Najeriya, EFCC na da izini na boye sunan wanda aka karbe dukiya da kadaorin na sata idan ana kan bincike a kansa, domin bayyana sunasa na iya shafar kokarin da ake na gano sauran kadarorin da ya mallaka ta haramtaciyyar hanya.