1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Wani harin kwanton bauna ya hallaka sojojin India a Kashmir

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 9, 2024

India da Pakistan sun jima suna zaman tankiya da juna, sakamakon kokarin kwace iko da yankin Kashmir da musulmi suka fi yawa a ciki.

https://p.dw.com/p/4i2dx
Hoto: AMIRUDDIN MUGHAL/EPA

Dakarun tsaron kasar India sun dukufa wajen farautar 'yan bindigar da suka yi wa ayarin sojinta kwanton bauna, tare da hallaka sojoji 5 a yankin Jammu da Kashmir da ke karkashin ikonta ranar Litinin.

Karin bayani:Jam'iyyar BJP a Indiya na son jan hankalin Musulmi a Kashmir

Ministan tsaron kasar Rajnath Singh, ya nuna bakin cikinsa da faruwar lamarin, wanda ya bayyana shi a matsayin harin ta'addanci, kuma ba za su saurara a kai ba, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

karin bayani:Pakistan ta bukaci MDD ta ja kunnen India

Ko a ranar Lahadin da ta gabata sai da masu tada kayar bayan suka hallaka sojojin India 3, yayin wata musayar wuta a kauyen Kulgat, ko da yake sun kashe masu boren guda 6, in ji rundunar 'yan sandan India.

India da Pakistan sun jima suna zaman tankiya da juna, sakamakon kokarin kwace iko da yankin Kashmir da musulmi suka fi yawa a ciki.