wani jirgin ruwa ya nitse a ƙasar Indiya
April 30, 2012Talla
Wani ƙasaitaccen jirgin ruwa da ke ɗauke da fasinjoji kimanin 250 ya nitse a wani teku da ke yankin arewa maso gabashin Indiya bayan da ya ci karo da wata mahaukaciyar guguwa. Jami'an 'yan sanda Assam da ke zama jihar da hatsarin ya faru a cikinta sun bayyana cewar mutane 35 daga cikin fasinjojin sun rasa rayukansu, yayin da wasu 15 suka yi batad damo.
A halin yanzu dai, mutane 50 ne aka ceto daga cikin wannan jirgin da ya nitse a tekun Brahmapoutre. Jami'an agaji na ci gaba da bincike da nufin ceto wasu fasinjojin ko kuma gano gawawwakin waɗanda hatsarin jirgin ruwan ya ritsa da su. Wannan katafaren jirgin ya nufin gundumar Fakirganjan lokacin da ya ci karo da wannan mahaukaciyar guguwar.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu