Wani jirgin sama na ƙasar Indiya ya yi haɗari
May 22, 2010A ƙalla mutane 160 suka mutu a cikin wani haɗarin jirgin sama da ya auku a kuɗancin ƙasar Indiya .Jirgin samfarin Boeing 737 na kamfanin Air indiya, wanda ya taso daga Dubai ɗauke da mutane 166, ya tarwatse ya yi ɗaya ɗaya bayan da ya kama da wuta,a sa'ilin dake kokarin sauka ya kuma zarce, daga kan hanyarsa.kilomita ɗaya kafin filin saukar jiragen sama na Mangalore wanda ke a yammacin Bangalore hed kwatar Karnataka.
yanzu haka dai wasu rahotanin dake zuwa da ke karo da juna na nuna cewa babu wani wanda ya tsira da ransa a cikin haɗarin yayin da waɗanda suka malaki kamfanin jiragen sama suke cewa mutane takwas sun sha a hadarin ,sai dai suna cikin wani halin mutu kwa kwai rai kwa kwai.
Mawallafi Abdourahamane Hassane
Edita Zainab Mohammed Abubakar
(