Wani malami zai yi zaman kaso a Birtaniya
September 6, 2016Wata kotu a Birtaniya ta yanke hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru biyar da rabi ga wannan malami da ke wa'azi na addinin Islama bisa laifin cewa ya na karfafa gwiwar magoya bayansa su tallafa wa mayakan IS.
Malamin mai suna Anjem Choudary dan shekaru 49 da ke zama fitacce cikin masu wa'azi a kasar ta Birtaniya tsawon shekaru, tun a watan Yuli ne dai mahukuntan na Birtaniya suka gurfanar da shi gaban shari'a saboda zargin cusa akida ta masu tsatstsauran ra'ayi da sunan addini.
Malamin dai ya sha hada gangami ko da yake ana kallon bai sabawa doka ba inda a wasu lokutan sukan je gaban ofishin jakadancin Amirka a ranar tunawa da harin 11 ga watan Satumba. Sai dai Choudary da ke zama haifaffen birnin na London ya fada rikici, bayan da aka gano sunansa cikin wadanda suka yi mubaya'a ga kungiyar ta IS, ko da yake malamin ya ce an yi rantsuwar ne ba tare da saninsa ba.