Labarin Wasanni: Kammala gasar tennis
June 12, 2023Ana dai fafata da gasar kofin zakarun nahiyar Turan duk shekara, kuma an fafata wasan karshen ne a filin wasa na Atatürk Olympic da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya. Wannan nasara ta kara fitowa fili da karfin da gasar Premier League ta Ingila ke da shi kamar yadda masharhanta suka nunar. Ita dai kungiyar Manchester City ta saka kwallo a raga ana mintoci 68 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ta kafar dan wasanta Rodri mai shekaru 26 da haihuwa dan kasar Spain.
An fara mayar da martani a Amurka bayan da shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Ajentina Lionel Messi wanda yake wasa da kungiyar PSG ta kasra Faransa, ya tabbatar da cewa zai koma kasar da wasa. Messi dai zai taka leda a kungiyar Inter Miami a kan makudan kudi. Haka kuma akwai talla da zai rinka yi wa wasu kamfanoni da zai kara samun kudin shiga.
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahly da ke kasar Masar ta samu nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Afirka, bayan ta doke kungiyar Wydad Casablanca. An dai tashi daga wasan daya da daya, sai dai kuma a fafatawar da suka yi a gida da waje kungiyar ta Al Ahly tana da ci uku yayin da ita kuma kungiyar Wydad take da maki biyu.#b#
Bayan kwashe tsawon makonni uku ana fafatawa a gasar tennis a birnin Paris na kasar Faransa da ake kira da Roland Garros ta shekara-shekara, a karshen Novak Djokovic ya yi nasara a bangaren maza yayin da Iga Swiatek ta samu nasara a bangaren mata. Shi dai Djokovic dan kasar Sabiya ya kasance cikin gwanayen wannan wasa na tennis, inda yanzu haka yake kan gaba cikin jerin gwanaye. Haka ita ma Swiatek 'yar kasar Poland, ta kasance wadda yanzu haka take jan zarenta a bangaren na tennis na duniya.
Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta Italiya wadda a baya ta lashe gasar Serie A da wasannin kasashen Turai, ta mika jinjina ga wanda ya mallaki kungiyar marigayi tsohon firaministan kasar Silvio Berlusconi. Shi dai Marigayi Berlusconi ya bar duniya yana da shekaru 86 kuma ya kasance daya daga cikin masu arziki na kasar. A cikin wata sanarwa kungiyar ta AC Milan ta ce, ko yaushe za ta tuna da shugabanta Marigayi Silvio Berlusconi wanda ya jagorance ta daga shekarar 1986 zuwa shekara ta 2017. A tsukin wannan lokacin, kungiyar ta lashe kambu 29 da suka hadar da gasar zakarun Turai da kuma lig din Italiya da ake kira da Serie A.