A wasannin Lig din Bundesligar kasar Jamus a wasannin mako na 18 bayan dawowa daga hutun lokacin sanyi. Ana a iya cewa illahirin manyan kungiyoyin kasar sun tako sa inda yaya babba Bayern Münich ta fara da nuna karfi ga Paderborn wacce ta iske ta har gida ta kuma casa ta da ci 4-1, yayin da Leipzig ta karbi bakuncin Union Berlin ta kuma doke ta da ci 3-1. Sai dai wasan da ya fi jan hankali a karshen mako a gasar ta Bundesliga, karawar da aka yi tsakanin kungiyar Augsburg wacce ta karbi bakuncin yaya karama Borussia Dortmund inda aka yi ruwan kwallaye har guda takwas.
Mai masukin baki ce dai ta fara zura kwallaye har biyu a jere kafin zuwa hutun rabin lokaci. To sai dai bayan an dawo daga hutun ta canza zane bayan da kungiyar Dortmund ta shigo da sabon dan wasanta Erling Haaland wanda ta cefano daga kungiyar Salzburg ta Ostriya makonni uku da suka gabata. Haalan ya yi nasarar shiga gasar ta Bundesliga da kafar dama inda daya bayan daya ya ci kwallaye har guda uku.
An kawo karshen wannan wasa yaya karama Dortmund na da ci biyar Augsburg na da ci uku kuma a karshen wasan mai horas da kungiyar ta Dortmund Lucien Favre ya bayyana farin cikinsa da wannan nasara da kuma musamman rawar da sabon dan wasan nasa ya taka a wannan karawa a karon farko.