Labarin Wasnni: Wasannin karshen mako
December 2, 2024A kasar Guinea Conakry da ke yankin yammacin Afirka inda ake alhini, bayan tabbatar da mutuwar kimanin mutane 56 sanadiyyar barkewar rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar kasar da yammacin wannan Lahadi da ta gabata, lokacin da ake tsaka da wani wasa da aka shirya don karrama shugaban mulkin sojin kasar Janar Mamadi Doumbouya. Akwai wasu 320 jikata. Akwai kuma tsaron alkaluman wadanda suka mutu sun zarce wadanda hukumomin suka tabbatar.
Likitoci da suka nemi a sakaya sunayensu, sun tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa asibitin birni na biyu mafi girma a kasar wato N'Zerekore ya cika makil da gawarwaki, wasu ma yashe a kasa, sakamakon cikar wuraren adana gawarwakin.
Wasu fayafayan bidiyo da aka rinka yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda fusatattun masu kallon wasan suka rinka gwabzawa da juna, har ma suka fantsama kan titunan birnin tare da kona ofishin 'yan sandan garin, don nuna fushinsu kan wani hukuncin da alkalin wasan ya yi a lokacin da kungiyoyin biyu ke fafatawa. Tuni Firamnista Mamadou Oury Bah na kasar ta Guinea ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matakan da suka dace na dawo da zaman lafiya. Tuni gayyaman jam'iyyun adawa suka ce gwamnati ke da alhakin abin da ya faru.
A wasannin lig na Bundealiga da aka kara a Jamus:
St. Pauli 3, Holstein Kiel 1
Bremen 2, Stuttgart 2
Freiburg 3, Monchengladbach 1
Augsburg 1, Bochum 0
Union Berlin 1, Leverkusen 2
Dortmund 1, Bayer Munich 1
Mainz 2, Hoffenheim 0
Heidenheim 0, Eintracht Frankfurt 4
Kuma wasan da Leipzig ta sha kaye a gida a hannun Wolfsburg 5 da 1.
Najeriya ta zama zakara a gasar wasanin motsa jiki na sojojin kasashen Afirka da aka gudanar a Abuja. Najeriya ta zo na daya inda ta samu lambobi yaboi 234 sai kasar Algeria da ta zo ta biyu da lambobi 96 yayin da Kenya ta zo matsayi na uku da lambobin yabo 50.
A wasan Kiriket da aka kara a karshen mako kasar Pakistan ta doke kasar Zimbabwe yayin karawa a birnin Bulawayo na Zimbabwe a karshen wannan makon da ya gabata.
Kasar Australiya ta haramta wa Matthew Richardson dan wasan tseren keken da ya samu lambar yabo a gasar Olympics shiga cikin wasannin tseren keken da za a gudanar na kasar ta Australiya, sakamakon yadda ya sauya sheka daga kasra ta Australiya zuwa Birtaniya. Hukumar kula da wasan tseren keken Australiya ta tabbatar da haka a wannan Litinin. Shi dai Matthew Richardson wanda aka haifa a Birtaniya, a watan Augusta da ya gabata ya bayyana komawa zama dan Birtaniya jim bayan ya samu lambar yabo a gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa.