Gwanjon rigar marigayi Diego Maradona
May 2, 2022A ranar Asabar din da ta gabata dubban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid suka yi ta tsallen murna a cibiyar kungiyar, bayan da ta doke Espayol da ci hudu da nema. Nasarar dai ta tabbatar da cewa kungiyar Real Madrid ta lashe gasar La Liga a bana, inda yanzu haka take da maki 81, yayin da Sevilla ke a matsayi na biyu da maki 64, kana Barcelona tana matsayi na uku da maki 63.
A wasan Bundesliga da aka gudanar a karshen mako kuwa, Augsburg ta sha kashi a hannun Cologne da ci hudu da daya. Kungiyar Bayern Munich da ke saman tebur da kuma aka tabbatar da ta sake lashe gasar a karo na 10 a jere, ta yi abin kunya inda ta sha kashi a hannun Mainz da ci uku da daya. Ita kuwa Stuttgart ta tashi wasa kunne doki daya da daya da kungiyar Wolfsburg, yayin da Dortmund ta yi abin kunya a gida ta hanyar shan kashi a hannun Bochum da ci uku da hudu. Arminia Bielefeld ta yi kunnen doki da takwararta Hertha Berlin daya da daya duka a mako na kusa da na karshe wato na 33 a kakar ta bana.
Shahararren dan wasan Tennis na duniya Rafael Nadal ya shiga sahun masu sukar matakin hana 'yan wasa daga kasashen Rasha da Belarus shiga gasar Tennis ta Wimbledon da ke wakana a Ingila duk shekara. Dan wasan dan asalin kasar Spain, ya bayyana matakin da rashin adalci ga 'yan wasan kasashen biyu da aka hana musu shiga sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine kuma take samun goyon bayan Belarus. Rafael Nadal ya ce a matsayinsa na dan wasa, yana jin irin yadda suke ji sakamakon hana su wasanni.
Babbar 'yar marigayi Diego Maradona da ke zaman tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Ajantina, ta ce rigar marigayin da za a yi gwanjo cikin wannan wata na Mayu ba asalin rigar da marigayin ya yi wasa da ita ba ce yayin wasan kusa da na kusa da na karshe a Ingila inda ya jefa kwallo da hannu a raga da ake yi wa lakani da "Hannun Ubangiji." Ita dai wannan riga ana sa ran za a sayar da ita kan milyoyin kudi, saboda yadda wannan wasan ya shahara. An yi wasan lokacin cin kofin duniya da Ajentina ta lashe a shekarar 1986 a kasar Mexiko, kuma Marigayi Diego Maradona ya taka rawar gani da bajinta fiye da tunani a lokacin wasan yayin da yake ganiyarsa.