1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Asibitoci sun sallami wasu

Uwais Abubakar Idris LMJ
April 3, 2020

A Najeriya ana kara samun mutanen da ke warkewa daga cutar Coronavirus, abin da ke samar da kyakkyawan fata na shawo kan annobar da ta karade duniya

https://p.dw.com/p/3aPE8
Symbolbild Hände waschen
Matakan kare kai daga CoronavirusHoto: Imago Images/M. Westermann

Ya zuwa yanzu dai mutane 20 cikin mutane sama da 184 da suka kamu da cutar a Najeriyar ne, aka bayyana cewa sun warke sumul kuma har an sallame su daga asibiti, abin da a zahiri ke samar da kwarin gwiwa da kwantar da hankali a tsakanin al'umma, musamman wadanda suka shiga cikin hali na tsoro da firgici kan cutar.

To sai dai a daidai lokacin da ake murna da samun nasara, tuni aka fara kira ga jama'a da su guji nuna kyama ga wadanda suka warke kuma suke komawa cikin al'umma, kamar yadda ake nuna kyama ga masu dauke kwayar cutar HIV/AIDs ko kuma SIDA, inda kwararru ke bayyana cewa akwai bukatar mayar da hankali wajen wayar da kan jama'a kan batun na gujewa nuna kyama. Kokari na ci gaba da bin ka'idojin da aka gindaya don yaki da yaduwar cutar ta Coronavirus dai, muhimmi ne ga alumma.