1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu 'yan Kenya sun gurfana a gaban kotun Yuganda

Halimatu AbbasJuly 30, 2010

An gurfanar da wasu 'yan Kenya a gaban kotu, bisa harin birnin Kampala.

https://p.dw.com/p/OYf0
Wani matashi Ba'amirke, da ya jirkata yayin harin da aka kai a Kampala.Hoto: picture-alliance/dpa

An gurfanar da wasu 'yan asalin ƙasar Kenya a gaban kotun majistare a Yuganda, bisa zargin aikata laifukan kisan kai har 76 da ke da nasaba da harin ƙunar baƙin wake da aka kai birnin Kampala a ranar 11 ga watan Juli. Mutanen da aka gurfanar ɗin dai sune, Hussaini Hassan Agad da Mohammed Adan Abdow da kuma Idris Magondu. Ana dai cajin su ne da hannu a wancan harin bama-bamai da ya halaka mutane da dama a wani wajen kallon wasan ƙwallon ƙafa na duniya da aka gudanar a Afirka ta Kudu. Tuni dai alƙalin kotun ya ba da umarnin a ci gaba da tsare su, kafin a miƙa shari'ar a gaban wata babbar kotu. Yanzu dai a ranar 27 ga watan Augusta ne dai mutanen uku za su sake gurfana a gaban kotun. Yanzu haka dai akwai 'yan ƙasar waje da dama da ake tsare da su dangane da wannan hari da ƙungiyar al-Shabab ta Somaliya ta ɗauki alhakin kai shi.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas