Moroko ta yankewa 'yan IS hukuncin kisa
July 18, 2019Talla
An kwashi sama da watanni uku ana shari'ar Abdessamad Ejjoud, wanda shi ya jagoranci fille kawunan matan da suka fito daga kasashen yankin Scandinavia. Masu shigar da kara sun dage kan a zartas da hukuncin kisan, duk da cewa, Moroko ta soke amfani da dokar tun shekarar 1993.
Matan biyu 'yan shekaru ashirin da hudu, sun gamu da ajalinsu ne a yayin wata ziyara da suka kai kasar ta Moroko a Disambar bara. Kungiyar IS dai ba ta fito fili ta amince da hannu a kisan ba sai dai wadannan da suka ce su 'yan kungiyar ne sun amsa laifukan kisan matan.