Watsi da tuhumar mataimakin shugaban Kenya
April 5, 2016Kotun hukunta masu manyan laifukan yaki ta duniya ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa William Ruto mataimakin shugaban kasar Kenya, wanda ake zargi da hannu a cikin tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shekara ta 2007. Alkalan kotun suka tabbatar da wannan mataki.
Mai magana da yawun kotun ta duniya Fadi El Abdallah ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar galibin alkalan kotun sun amince da matakin watsi da tuhumar ake yi wa mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto gami da wani dan jarida Joshua arap Sang.
Tuni aka fara mayar da martani kan matakin inda Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ta Kenya, wanda shi kansa aka kori karar da aka kai shi, ya yi maraba da hukuncin kotun, amma lauyan wadanda aka zalunta ya yi tir da matakin kotun.