Corona za ta wahalar da wasu kasashen Afirka
April 9, 2020Talla
Michel Yao, babban jami'in WHO a Afirka shi ne ya yi wannan gargadin a ranar Alhamis, yana mai cewa idan har aka ci gaba da tafiya a irin yadda ake a yanzu to Afirka za ta samu yawaitar annobar Coronavirus kamar yadda ake gani a kasar China da nahiyar Turai. Sai dai bai bayyana sunayen kasashen da za a samu yawaitar annobar ba.
Kawo wannan lokaci kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce akwai kusan mutum 11,000 da ke da cutar Corona a Afirka, cutar ta kuma yi ajalin mutum 562 a kasashen Afirka.