1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta ayyana cutar Zika a matsayin barazana ga duniya

Abdourahamane HassaneFebruary 1, 2016

Ƙwararru na Hukumar Lafiya ta duniya WHO sun bayyana cutar Zika a matsayin wadda ke bukatar agajin gaggawa na ƙasa da ƙasa.

https://p.dw.com/p/1HnIF
Schweiz WHO zu Zika Virus
Hoto: Reuters/P. Albouy

Taron wanda aka soma a yau ta waya tarho tsakanin jami'an Hukumar ta WHO da kuma wasu ƙasahen a ciki har da Brazil da Argentina waɗanda cutar ta shafa sun ce akwai buƙatar ƙasahen duniza su farka tun da sauran wuri domin zaƙar cutar

mutane miliyan uku zuwa huɗu ne ke fama da cutar a yankin Latine Amirka,wacce sauro ke zaman sanadinta wadda kuma ke janyo nakasa ga jarirai da aka haifa.Tuni da ƙasashen Kwalambiya da Salvador da Equador da Brazil da Jamaica da Porto Rico suka gargaɗi mata da kada su kuskura su samu juna biyu inda har ba a shawo kan wannan cuta ba ta Zika.