1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar daukar matakai kan cutar Zika

Lateefa Mustapha Ja'afarFebruary 3, 2016

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci da a rinka yin amfani da matakan kariya yayin saduwa domin gujewa yaduwar kwayar cutar Zika.

https://p.dw.com/p/1HpPw
An bukaci daukar matakai don kare kai daga kamuwa da kwayar cutar Zika.
Daukar matakai a kan kwayar cutar Zika.Hoto: Reuters/P. Whitaker

Hukumar ta WHO wadda ta nuna damuwarta dangane da sabon rahoton da ya fito dangane da kwayar cutar ta Zika a Amirka, wanda ya tabbatar da cewa ana kamuwa da ita ta hanyar saduwa, ta kuma bukaci a kara zurfafa bincike a kan cutar da sauro yafi yada ta. Da yake zantawa da manema labarai, kakakin hukumar ta WHO Christian Lindmeier ya ce ya zamo wajibi su yi wannan gargadin ganin cewa an samu wadanda suka kamu da cutar ta hanyar saduwa.

Mr. Lindmeier ya ce "mutane biyu ne kacal muka gani wadanda suka kamu da cutar ta hanyar saduwa, wanda hakan ke nuni da cewa cutar za ta iya yaduwa ta hanyar maniyi ko kuma jini ko da ya ke kalilan ne wadanda suka kamu da cutar ta hanyar saduwa, wanda suka kamu da ita ta hanyar sauro sun fi yawa."