Kwanaki 100 na sabon shugaban Kenya
December 22, 2022Daga cikin alkawuran da Shugaba William Ruto ya yi wa 'yan kasar ta Kenya dai, akwai batun rage tsadar rayuwa ta hanyar zaburar da harkokin tattalin arziki. Shugaba Ruto dai ya samu yabo daga bangaren shari'ar kasar, bayan karin girman da ya yi wa wasu manyan alkalai su shida da shugaban da ya gada Uhuru Kenyatta ya yi watsi da daga darajarsu duk da shawarar da ma'aikatar da ke kula da alkalai da ayyukan shar''a ta bayar. Shugaba Ruto ya kuma yi alkawarin aiki kafada da kafada da bangaren shari'ar domin tabbatar da wanzuwar adalci a kasar, kuma a fadar Eric Theuri shugaban kungiyar lauyoyin kasar ta Kenya bai saba alkawarin ba cikin kwanakinsa 100 a kan madafun iko. To sai dai 'yan kasar da dama musamman kungiyoyin kare hakkin dan Adam, na dari-dari da majalisar ministoci da ma bangaren shari'ar.
Baya ga fannin na shari'a dai Shugaba Ruto ya yi alkawarin rage tsadar rayuwa tare da samar da jari ga matasa, alkawuran da wadanda abin ya shafa suka ce sam bai cika su ba. Sai dai kuma ra'ayoyi sun sha bam-bam a bangaren masana da masharhanta, inda Farfesa Fred Ogola kwararre ne a kan harkokin tafiyar da gwamnati ke cewa Shugaba Ruto bai burge shi ba a kwanaki 100 da ya yi a karagar mulkin Kenyan. To amma ga Janet Ouko wata mai sharhi kan harkokin ilimi da shugabanci, fannin ilim dai sai san barka cikin wadannan kwanaki na Shugaba Ruto ko da yake abu ne da ke matsayin kada-ran kada-han. Shugaban dai na ci gaba da shan matsi kan yadda rayuwa ke kara tsanani ganin da bakinsa ya ce zai dauki mataki a kan matsalar. Abin da mutane ke son gani shi ne rage farashin man fetur da na kayan masarufi, amma maimakon samun hakan sai tashi suka yi musamman ma bangaren sufuri.