1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Xi Jinping zai dore a wa'adi na uku a China

Abdoulaye Mamane Amadou Zainab Moh' Abubakar
October 23, 2022

A karon farko cikin tarihi shugaban China Xi Jinping zai dore a wa'adi na uku na mulkin kasar bayan da babban taron jam'iyyar Kwaminisanci ya sake zabar shi a matsayin shugaba.

https://p.dw.com/p/4IZAn
China Peking | Parteitag der Kommunistischen Partei
Hoto: Andy Wong/AP Photo/picture alliance

Taron kolin jam'iyyar Kwamisancin a China ya zabi shugaban kasar Xi Jinping a wani sabon wa'adi na uku na shugabanci jam'iyyar, wanda hakan ka ba shi damar cigaba da tafiyar da harkokin mulki, abin da ke zaman na farko a tarihi.

Bayan Shugaba Jinping, taron ya kuma zabi wasu da ake ganin na hannun damansa hudu a mukamai mabanbanta don tafiyar da harkokin jam'iyyar da ma mulki. A cikin watan Maris na 2023 ake sa ran taron kwamitin zartarwar jam'iyyar Kwamisancin ya zabi Li Qiang shugaban Shanghai a matsayin sabon firaminista inda zai maye gurbin Li Keqiang.

Wasu da suka hada da Ding Xuexiang da Li Xi shugaban jam'iyyar a lardin Guangdong na daga cikion wadanda aka nada a manyan mukamai na tafiyar harkokin mulki.