Yaduwar rikicin Sudan a yankin Sahel
May 8, 2023Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a Sudan, inda bangarorin da ke cikin rikicin suka sha take yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma. Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da wani gagarumin bala'i na jinkai da ka iya yaduwa a yankin kusurwar Afirka. Sai dai akwai fargabar cewar, ba wai kawai matsalar za ta shafi wannan yanki kadai ba ne, akwai yiwuwar yaduwarsa zuwa yankin Sahel mai fama da rigingimu na masu tayar da kayar baya.
Matsanancin halin da ake ciki yana da sarkakiya saboda rashin sanin yadda za a magance tashe tashen hankula, in ji Henrik Maihack, shugaban sashen Afirka na gidauniyar Friedrich Ebert:
"Matsalar wannan yanki sau da yawa shi ne cewa babu wani tsari na gama-gari, wato tsaro na bai daya, amma a ko da yaushe ana shirya tsaro a tsakanin kasashe daban-daban, ta yadda kasashe makwabta ko kungiyoyin da ke dauke da makamai a daya bangaren na iyakoki su tsoma baki cikin kowane lamari a rikice-rikicen, wanda ke sa ka'idojin rikici ko karewa ya fi wahala."
Rikicin Sudan dai na barazanar kara kwararar kananan makamai ta kan iyakokin kasar zuwa wasu kasashe, wadanda za su iya isa yankin Sahel musamman Mali da Nijar da Burkina Faso kamar yadda kwararru a kan lamuran Afirka suka nuna fargaba. Dama dai akwai kungiyoyi masu dauke da makamai, kuma sabbin makamai za su haifar da tabarbarewar yanayin tsaro.
Wannan kuma ya kara rura wutar matsalar tallafin jinkai, wanda tuni ya ke fuskantar wani yanayi saboda rashin isasshen kudade a Somalia da Sudan da kuma Sudan ta Kudu, lamarin da ka iya ta'azzara sakamakon fadan da ake yi a Sudan.
Yanzu haka dai dubban mutane na ci gaba da kaurace wa kasar ta Sudan domin neman mafaka a kasashe makwabta, kuma akasarinsu mata ne da kananan yara wadanda ke tafiya a kafa ba tare da wani tanadi ba a cewar mai magana da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Eujin Byun.
"Fiye da kashi saba'in cikin dari na 'yan gudun hijirar da ke tsallakawa kan iyaka a halin yanzu mata ne da kananan yara. Wadanda ke tafiyar tsawon sa’o’i 24 a kafa, ba su da komai a tare da su, kuma sun isa kan iyakar babu matsuguni, babu tufafi, babu abinci, balle ruwa. Don haka wannan ita ce bukatar gaggawa da muke neman daga kasashen duniya."
Kasar ta Sudan wadda ta kasance ba ta da kwanciyar hankali tsawon shekaru a siyasance, na fuskantar rikicin madafan iko tsakanin manyan hafsoshin soja biyu da rundunoninsu, watau dakarun Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke yaki da mayakan RSF na Mohammed Hamdan Daglo.
Barkewar rikicin na Sudan dai ya jefa kasashen da ke makwabtaka da ita cikin wani hali, kasar da ita kanta ke zama mai rauni sosai a fannin tattalin arziki, sannan kuma a karkashin mulkin soji. Yanzu haka kuma, 'yan gudun hijira daga Sudan na kwarara zuwa kasashen Sudan ta Kudu da Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da wasu kasashe masu nisa kamar Masar da Saudi Arabiya.