Yahya Jammeh ya kafa dokar ta baci
January 17, 2017Talla
Lamarin ya biyo bayan yunkurin sassanta rikicin cikin ruwan sanhi da Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta gaza cimma wacce ke shirin daukar matakin yin amfani da karfin soji.A halin da ake ciki rahotannin daga kasar ta Gambiya na cewar gwamnatin ta Jammeh na ci gaba da tsare wasu sojojin wadanda ba su amince ba da shugaban ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki.A ranar Alhamis mai zuwa yakamata shugaba Jammeh ya sauka ya mika mulki ga Adama Barrow mutumin da ya lashe zaben wanda yanzu haka yake yin hijara a Senegal.