Yaki da hukuncin kisa a kasar Gambiya
October 10, 2012A nahiyar Afrika, daga cikin kasashe 54, guda 38 sun soke hukuncin kisa. Zartar da hukuncin kisa da aka yi kan wasu mutane a kasar Gambia da ke Afirka ta yamma a karshen watan Agusta, ya haddasa kararraki a ko ina a duniya. Kasar dai tun shekara ta 1981 bata zartar da irin wannan hukunci mai tsanani ba, ko da shike ta yi kaurin suna game da take hakkin 'yan Adam karkashin mulkin shugaban kasa Yahya Jameh. Duk da haka zartas da hukuncin kisa kan wasu mutane 'yan kurkuku tara a karshen watan Agusta ya zo a wani hali na ba-zata ga kasashe da kungiyoyin duniya. Lisa Sherman Nikolaus ta kungiyar Amnesty International ta na daga cikin wandanda suka baiyana damuwa.
"Mutane ana yanke masu hukuncin kisa saboda laifukan da aka ce sun aikata na siyasa ko cin mutuncin kasa, abin da bai dace da dokokin duniya ba. Muna samun labarai na azabtarwa da kuma tauye hakkin jama'a na fadin albarkacin bakinsu. Wato a takaice, akwai matakai masu yawa na danne hakkin jama'a dake kawo mana damuwa."
Salon azabtarwa da ke kama da aiwatar da hukuncin kisa a Gambiya
Shugaba Yahya Jameh ya karbi wannan mukami ne sakamakon juyin mulki a shekara ta 1994. Tun daga wannan lokaci ya ke ci gaba da kokarin ganin ya kawar da 'yan adawa a duk inda suke. 'Yan adawar dake tsare, akan kai su wani sansani da ake kira wai Mile 2 Central a ci gaba da tsare su, abin da daidai yake da hukuncin kisa, inji Banka Manneh, shugaban hadaddiyar kungiyar kare hakkin jama'a ta Gambia.
"Yadda ake tsare da fursunoni a sansanin na Mile 2 Central abu ne da ko kadan bai dace da rayuwar dan Adam ba, saboda a karshe ko dai mutum ya mutu ne a wannan wuri ko kuma daga baya irin azabar da mutum ya sha a sansanin ya kashe shi. Sau tari, sojoji da jami'an tsaro akan yanke masu hukuncin kisa ko daurin rai da rai a kasar ta Gambia. Abincin sansanin bashi da kyau, inda mutum yakan kamu da cutukan dakan kashe shi cikin hali na azaba mai tsanani."
'Yan kasashen waje na daga cikin wadanda aka kashe a Gambiya
Daga cikin mutanen da aka zartas da hukuncin kisa kansu a watan Agusta har da guda biyu masu rike da paspo na Senegal. Hakan ya sanya mutane masu yawa su kai ta zanga-zanga a makwabciyar kasar ta Senegal domin adawa a hukuncin na kisa. Banka Manneh yayi tsokaci ya na mai cewa:
"A baya-bayan nan 'yan kasar sun fara nuna karin karfin zuciya. 'Yan Gambia sun lura da yadda al'ummar Senegal suka tashi tsaye har suka tabbatar da ganin an sami canjin gwamnati a kasarsu, suna kuma lura da juyin juya halin dake gudana a kasashen Larabawa. Wadannan abubuwa sun sanya al'ummar na Gambia tunani mai zurfi, tare da nuna cewar watakila duk yadda ake zaton ba zasu iya tabuka komai ba, a zahiri al'amarin ba haka yake ba."
Barazanar ladabtar da Gambiya idan ba ta yi watsi da kukuncin kisa ba
Kamar yadda Manneh ya nunar, an zartas da hukuncin kisan ne tare da manufar kara tsoratar da al'ummar Gambia. Saboda haka ne kasashe da kungiyoyin duniya suka yi wa Gambia barazanar takunkumi, tare da yin kira ga shugaba Jameh ya kiyaye dokokin kasa da kasa. Su ma kungiyoyin kare hakkkin 'yan Adam sun yi Allah wadai da zartas da hukuncin kisa a Gambia. Hakan ya sanya gwamnati ta dakatarda shirin da tayi na aiwatar da hukuncin kisa kan karin mutane 38 da aka shirya yi a tsakiyar watan Satumba, ko da shi ke majalisar dokokin kasar ta yi magana ne a game da dakatar da hukuncin kawai. Ko da shi ke Manneh yayi marhabin da wannan mataki, amma bai cire tsammanin zuwa gaba za'a kashe wadannan mutane ba. Yace gwamnati ta yi magana game da hukuncin ne, abin da ke nufin ta na iya zartas da shi a duk lokacin da take so. Duk kuma wanda ya san Yahya Jameh da take-takensa tun da ya kama mulki, zai san cewar ran dan Adam ba a bakin komai yake ba gareshi.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou awal